
Hukumar ‘yansandan Najeriya ta musanta cewa an ga jami’anta suna kwasar man fetur bayan da wata tankar mai ta fadi.
Bidiyo ya watsu sosai inda aka ga wasu da kayan ‘yansandan suma sun shiga sahu masu satarman daga tankar.
Saidai a sanarwar da kakakin hukumar ‘yansandan ta kasa, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, yace ba ‘yansandan Najeriya ne ba a bidiyon, ‘yansandan makwabtan Najeriya ne.
Ya kara da cewa, an saki Bidiyonne kawai dan a batawa hukumar ‘yansandan Najeriya suna.
Yace jami’an tsaron dake bidiyon, faransanci suke ba Turanci ba yace dan haka ba ‘yansandan Najeriya bane.
Yace hukumar ‘yansanda tana nan kan gudanar da aikinta bisa doka da kwarewa. Ya gargadi mutane su daina yada labarin da bai inganta ba.