
Rahotanni sun bayyana cewa, Bankin Duniya ya baiwa Najeriya kyautar Dala Miliyan $10.5.
Bankin ya bayar da kyautar ne dan amfani da gudin wajan inganta ayyukan babban bankin Najeriya, CBN dan ya karfafa bangaren fasahar zamani.
A baya dai an bayyana wadannan kudade a matsayin bashi ga Najeriya.
Saidai binciken jaridar Punchng ya tabbatar da cewa kudin kyautane kamar yanda wata majiya daga bankin Duniyar ta gayawa jaridar.