
Babban Bankin Duniya (World Bank) ya nada Aliko Dangote tare da wasu manyan ‘yan kasuwa da masana daga sassa daban-daban na duniya zuwa mukamai na musamman a wani sabon kwamiti da aka kafa domin karfafa ci gaban tattalin arziki da rage talauci.
An bayyana cewa wannan nadin na nuna yadda Bankin Duniya ke daraja ƙoƙarin da Dangote ke yi wajen bunkasa masana’antu da kuma tallafa wa ci gaban al’umma musamman a nahiyar Afirka.
Baya ga Dangote, akwai wasu fitattun mutane da suka haɗa da shugabannin kamfanoni, masana tattalin arziki, da wakilan ƙungiyoyin kasa da kasa da za su yi aiki tare da bankin domin samar da hanyoyin warware matsalolin da ke hana ci gaba a duniya.
Wannan ci gaba na daga cikin shirin Bankin Duniya na samar da tsayayyen tsarin ci gaba mai dorewa da kuma jawo hankalin masu zuba jari zuwa kasashen da ke tasowa.