
Wani Rahoto da babban bankin Najeriya, CBN ya fitar yace, Bankukan Najeriya sun rufe rassa 229 a fadin kasar saboda raguwar yawan mutanen dake zuwa bankunan.
Rahotan yace yawanci mutane na zuwa POS ne dan cirewa ko saka kudi maimakon su shiga Banki.
Rahoton ya kara da cewa, an saka kudi sau 5,373 a shekarar 2023 inda a shekarar 2024 kuma aka saka kudi sau 5,144 wanda hakan ke nuna cewa yawan kudaden da ake sakawa a Bankuna sun ragu.