Friday, December 5
Shadow

Barayin waya sun kashe ma’aikacin Jami’ar Northwest ta Kano

Masu kwacen waya sun kashe wani ma’aikacin Jami’ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daba masa wuta.

Bayanai sun nuna cewa barayin sun ritsa shi ne a yankin unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso, inda suka sossoke shi da wuka a ciki kuma suka kwace wayarsa, a ranar Laraba.

Marigayin ya rasu bayan da aka garzaya da shi asibitin koyarwa na Mallama Aminu Kano, a jiya Juma’a.

Shugaban kungiyar ma’aikatan jami’ar (NASU), Kwamared Bashir Muhammad, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya yi kira ga gwamnatin jihar kano da sauran hukumomi da su dauki tsattsauran mataki a kan kisan.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yanda wata masoyiyar tauraruwar fina-finan Hausa, Amal Umar ta je ta fashe da kuka saboda irin son da take mata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *