Wednesday, May 28
Shadow

Barazanar rufe Facebook ta ficewa daga Najeriya ba zai hana mu hukunta su ba – Inji Gwamnati

Hukumar da ke sanya ido kan farashi da kare haƙƙin masu sayen kaya ta Najeriya (FCCPC), ta ce barazanar da kamfanin Meta ya yi na ficewa daga ƙasar, ba zai hana a hukunta shi ba.

Hukumar ta ce ba za a janye shari’ar da ake yi da Meta ba duk da barazanar da ya yi.

FCCPC ta ce kamfanin ya yi barazanar ficewa daga Najeriya ne domin a ji tausayinsa, da kuma matsawa hukumar canza matakin da ya ɗauka na cin tarar kamfanin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da darektan hukumar, Ondaje Ijagwu ya fitar ranar Asabar.

Hakan kuma na zuwa ne bayan wani gargaɗi da Meta ya yi da farko cewa “za a tilasta masa rufe shafukan Facebook da Instagram a Najeriya don kauce wa barazanar fuskantar hukunci”.

Karanta Wannan  Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Dr. Dalhatu Bafarawa ya koka da rashin kishin kasa na 'yan siyasa

Hukumar ta zargi Meta da yi wa bayanan ƴan ƙasar kutse, ciki har da aika bayanan ba tare da izininsu ba da rashin mutunta masu amfani da shafukan kamar yadda ake yi a sauran ƙasashe da kuma ɓullo da tsare-tsare da ba su da kyau kan ƴan ƙasar.

A bara ne hukumomin sanya ido uku na Najeriya suka lafta wa kamfanin tarar da ta kai fiye da dala miliyan 290, bisa zargin kamfanin da karya wasu dokoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *