Barr. Abba Hikima Fagge: “Shugabannin siyasa ne ke hura wutar faɗan daba a Kano”

Fitaccen lauya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Kano, Barrister Abba Hikima Fagge, ya yi tsokaci kan matsalar fadan yan daba da ke ta ƙara ƙaruwa a cikin birnin Kano. A cewarsa, ba matasa da kansu ne tushen wannan matsala ba, sai dai shugabannin siyasa da ke amfani da su wajen cimma muradunsu.
Barr. Abba ya bayyana cewa, a lokutan siyasa musamman, ana yawan ganin yadda ake rarraba kuɗi da miyagun ƙwayoyi ga matasa domin a tura su wajen tada tarzoma, abin da daga ƙarshe yake jefa al’umma cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali.
Ya ƙara da cewa, “Matsalar daba ba sabon abu ba ne a Kano, amma abin takaici shi ne yadda shugabannin da ake ɗora ran samun mafita a kansu suke ƙara ƙara wa matsalar wuta. Sai ka ji an raba makamai, an ɗauki hayar matasa a matsayin sojojin siyasa, abin da daga baya ya zama barazana ga kowa da kowa, har da wadanda suka haifar da lamarin.”
Barr. Abba Hikima ya shawarci gwamnati da jami’an tsaro da su ɗauki mataki cikin gaggawa, tare da hukunta manyan masu ɗaukar nauyin yan daba, ba wai kawai a tsaya da tarwatsa matasa a titi ba. Haka kuma ya bukaci iyaye da malamai da su tashi tsaye wajen tarbiyyar yara tun daga tushe, domin rage wa siyasa damar amfani da su.
Ya kammala da cewa: “Idan ba a dauki matakin da ya dace ba, matsalar fadan daba za ta ci gaba da zama barazana ga rayuwa da dukiyoyin al’umma a Kano.