
Tsohon Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Solomon Dalung, ya ce ‘yan siyasar da suka fice daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki suna yi ne kawai domin neman a share laifukansu ne na almundahana.
Dalung wanda ya bayyana hakan ne a Abuja inda ya nuna rashin gamsuwarsa da cewa ’yan siyasa suna tururuwa zuwa jam’iyyar APC ne saboda ta yi aiki mai kyau, ko dan farin jininta da yi wa talaka aikin da ya dace.
Dalung ya ce masu sauya shekar suna la’akari da kalaman tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole da ya ce komai girman zunubansu, za a gafarta musu da zarar sun koma APC, ko da yake Oshiomhole ya musanta wannan magana da aka danganta shi da ita.