Friday, December 5
Shadow

Bayan Allah sai Tinubu a gurina, dan ko iyalina, da mahaifana basu kaimun Tinubu ba>>Inji Ministan Ayyuka, David Umahi

Ministan Ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa, bayan Allah sai Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a wajensa.

Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a Abakaliki yayin da yake bayyana irin jinjina da amincin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bashi.

Yace yabon da shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu ya masa yafi mai a bashi Dala Tiriliyan daya.

Yace kuma a kullun yana fada idan har ya dora iyalinsa ko danginsa a sama da Allah ko Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu to kada Allah ya biya masa bukatunsa.

Karanta Wannan  Ko Kunsan cewa, 'Ya'yan El-Rufai da David Mark wanda shine shugaban jam'iyyar Gamayyar 'yan Adawa ta ADC duka 'yan APC ne?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *