Friday, December 5
Shadow

Bayan da suka ta yi yawa, Ministan Abuja, Nyesom Wike yace baya dana sanin Sakawa babban dakin Taron Najeriya sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

‘Yan Najeriya, Musamman kungiyoyin fafutuka, sun yi Allah wadai da sakawa babban dakin taron Najeriya dake Abuja sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya canjawa babban dakin taron sunane bayan da ya gyarashi.

An gano akalla gurare 7 da suka hada da barikin sojoji da filin jirgin sama da sauransu wadanda aka sakawa sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Lamarin yasa abin ya fara damun mutane musamman masu fafutukar kare hakkin al’umma suka fara suka.

Saidai a martaninsa, Wike Ya bayyana cewa duk me suka ya je yayi ta yi, yace ya ji wasu na cewa, wai ba Tinubu ne ya gina dakin taron ba.

Karanta Wannan  Hotuna Gwanin ban Tausai na wata likita bayan masu Gàrkùwà da mutane sun sakota

Yace to gurare da yawa da aka sakawa sunayen manyan mutane, kamar su Filin jirgin sama na Murtala Muhammad da Nnamdi Azikwe ai duk ba su ne suka ginasu ba.

Yace dan haka bai yi dana sanin saka sunan ba kuma mutane idan mutuwa zasu yi su je su mutu shi dama mun yi yawa a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *