
Sanata Ahmed Aliyu Wadada daga Jihar Nasarawa ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar SDP.
Ya bayyana cewa dalilinsa na barin jam’iyyar shine ba zai iya ci gaba da zama da wadanda basu da akida a jam’iyya daya ba.
Ya bayyana hakanne a hirarsa da ‘yan jarida inda yace Musamman Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, yace bashi da akida.
Yace El-Rufai na kan gaba wajan jawo hankalin mutane da cewa ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya.
Ya kara da cewa shine ya ce a zabi Tinubu amma saboda bai samu mukamin Minista ba amma ya bar jam’iyyar.