
Hukumar mulkin soji ta kasar Burkina Faso tace tana rike da sojojin Najeriya 11 bayan da jirginsu yayi saukar gaggawa a Bobo-Dioulasso dake Burkina Faso.
Hukumar tace ta dauki wannan mataki da cewa kutsene Najeriya take shirin yiwa kasar dan jirgin ya shiga sararin samaniyar ta ba tare da izini ba.
Kuma tace hukuncin wannan laifi shine Kisa.
Hukumar kasar Burkina Faso tace ta baiwa sojojinta umarnin duk jirgin da ya shigo mata kasa ba da izini ba kawai a bude masa wuta ba wani jiran ba’asi.
Rahotanni sun ce jirgin sojin Najeriyar ya keta ta sararin samaniyar Burkina Faso ne akan hanyarsa ta zuwa kasar Senegal.