
Farfesa Usman Yusuf ya bayyana cewa, Kaso 80 na matsalar Najeriya gwamnoni ne.
Yace Gwamnonin basa gayawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gaskiya.
Yace shugaba Tinibu yace ya basu kudin tallafi a saukakawa mutane rayuwa amma babu abinda suke yi.
Yace akwai yunwa a Najeriya inda yayi kira ga shugaban kasar yayi wani abu.
Farfesa ya bayyana hakane a wata hira da Trust TV ta yi dashi.