
Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana yanda ta tsira daga hannun ‘yan Damfara.
Mansurah tace wani yaro ya je gidanta inda ya rubuta sunanta a jikinsa da sunan cewa, wai yana sonta, yana son ta taimaka masa.
Saidai tace ta kai maganar wajan ‘yansanda inda aka mayar da yaron Bauchi saboda yace daga kauyen Bauchi ya fito, tace ta yi yunkurin tallafawa yaron inda tace a tambayo kudin makarantar Bokonsa da Arabi.
Tace amma sai akance wai makarantar Arabi ana biyan Naira dubu 70 duk wata ita kuma Boko ana biyan Dubu 150 duk wata.
Mansurah tace data ga abin nasu damfara ne sai kawai ta ce a bar maganar ta daina kulasu.
Tace kwatsam sai gashi kuma ta ga yaron wai ya rubuta sunan Lilin Baba a jikinsa.
Mansurah tace Allah ya ceceta.
Kalli Bidiyon ta:
Akan samu masoya shahararrun mutane na gaskiya sannan ana kuma haduwa da ‘yan Damfara irin wannan.