
Tauraruwar fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa ta bayyana cewa, ta taba aure, ta bayyana hakanne a hirar da Hadiza Gabon ta yi da ita a shirinta me suna Gabon Show.
Samha ta bayyana cewa, ‘yan matan da zawaranwan wannan zamanin duk daya ne sai wadda Allah ya tsare.
Samha ta kuma bayyana cewa, ita tana son diyarta ta gajeta dan ta san rayuwa me kyau ta ke yi.