
A baya ne dai wani mutum ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda aka ji labarin cewa wai ya taho a kafa tun daga Legas dan ya je ya ga Naziru Sarkin Wakar.
An hadashi da yaron Sarkin Wakan inda ya rika masa Hidima ya kama masa otal aka ajiyeshi ya rika bashi abinci har zuwa ranar da suka hadu da sarkin Wakar.
Saidai da ya tashi tafiya gida, ya nemi yaron sarkin wakar sai ya hadashi da Sarkin Wakan ya gaya masa cewa, zai tafi, inda yace yana zarginsa ne Sarkin Waka ya bada kudi a bashi amma yaki bashi.
Lamarin ya kaisu ga har ofishin ‘yansanda saidai an bada hakuri an sasanta.
Daga karshe yaron Sarkin Wakan ya bashi Naira dubu dari biyu yace inji sarkin Waka amma yace yaga alamar ya raina.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai.
Da yawa akan samu wasu dake attaki a kafa daga gari me nisa dan zuwa su ga masoyansu.