
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa jihar Anambra inda yake ziyarar aiki a yau, Alhamis.
Shugaban iya isa filin sauka da tashin jiragen sama na Chinua Achebe dake jihar inda ya samu tarbar gwamnan jihar, Charles Soludo da ‘yan majalisar jihar da sauran dattawan jihar.
Shugaba Tinubu kuma ya samu ya tsaya an masa taken Najeriya inda sojoji suka yi harbi sama dan girmamashi.
Bayannan kuma, Shugaba Tinubu ya shiga motar da aka tanada dan shi tare da Gwamnan jihar inda zai zarce dan fara kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta gudanar.