
Wani mutum me suna Yunusa Ahmadu Yusuf ya rigamu gidan gaskiya bayan shiga dakin Otal da wata mata me suna Ruth.
Lamarin ya farune a Karu-Jikwoyi, Abuja inda mutumin me shekaru 47 ya mutu.
Rahotanni sun ce tun bayah da ya shiga daki da matar bai ci komai ba sai giya yake ta kwankwada.
Matar ta fita ta sayo masa lemun kara karfin kwanji inda bayan ya sha ne ya suma, daga nan ne kuma rai yayi halinsa.
Tuni an fara binciken dalilin mutuwarsa.