Saturday, December 13
Shadow

Bisa satar Naira miliyan 360, kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin shekaru 74 a gidan yari

Wata babbar kotu da ke Ajah, a jihar Lagos, ta yanke wa Chukwudi Okonkwo Goodness, hukuncin daurin shekaru 74 a gidan yari bisa laifin satar Naira miliyan 360 da kuma bayar da takardun cirar kudi a asusun bankin da babu kuɗi a cikin sa.

An gurfanar da Goodness ne a shekarar 2016 bisa tuhuma 33 da hukumar EFCC ta shigar. An ce ya karkatar da kuɗin ne daga wani mutum mai suna Henry Nnadike a Ikeja tsakanin watan Yuni da Yuli, 2015.

Bayan shari’ar da ta ɗauki tsawon shekaru tara, mai shari’a Josephine Oyefeso ta same shi da laifi a kan tuhume-tuhume 32.

Bayan haka an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a kan tuhuma ta sata, sannan shekaru biyu-biyu a kowace tuhuma daga cikin sauran tuhume-tuhume da suka shafi bayar da katin cirar kudi a asusun da babu kuɗi a cikin sa.

Karanta Wannan  Bidiyo: An yi kuskuren turawa Fasto Naira Miliyan 1 mimakon dubu dari a matsayin sadaka saidai da aka ce ya mayar da kudin, yace Kudin da aka baiwa Yesu sadaka ba'a mayar dasu, me kudin ya kira 'yansanda

Haka zalika, an sake yanke masa hukuncin shekaru bakwai a tuhuma ta ƙarshe.

Kotun ta kuma umarce shi da ya mayar da Naira miliyan 215 ga mamallakan su a cikin kwanaki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *