Thursday, April 17
Shadow

Bobrisky ya shigar da ATM gidan yari ta barauniyar hanya ya cire Naira Miliyan 35 inda ya baiwa ma’aikatan gidan yarin cin hanci suka barshi ya yi ta bushasha

Rahotanni sun bayyana cewa, shahararren dan daudu, Bobrisky ya shigar da ATM guda 8 cikin gidan yari a lokacin da ake tsare dashi inda yayi Amfani da POS ya cire Naira Miliyan 35 ya baiwa ma’aikatan gidan yarin cin hanci dan su barshi yayi rayuwar jin dadi a gidan yarin.

Basaraken kirikiri, Chief Babalola Shabi ne ya bayyana hakan a wajan wani taron karawa juna sani da hukumar ‘yansandan jihar Legas ta shirya.

Basaraken ya kara da cewa, Bobrisky be yi zaman gidan yarin da aka kaishi ba, maimakon hakan, an kaishi wani gidane a wajen gidan yarin bisa yaddar wasu gurbatattun ma’aikatan gidan yarin.

Karanta Wannan  Najeriya ta ƙara yawan man da take haƙowa - Rahoto

Ya bayyana cewa da taimakonsa ne aka gano cewa Bobrisky bai yi zaman gidan yarin ba inda yace sai da ya tara masu sana’ar POS na yankinsa sannan ya kira hukumar EFCC dan ta bincika ta tabbatar da wannan zargi.

Yace an dakatar da ma’aikatan gidan yarin da suka taimakawa Bobrisky da aikata wannan ta’asa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *