
Buhari wani Mala’ika ne da ya zo a siffar mutane – Akande
Chief Bisi Akande mai mallakin jam’iyyar APC Kuma tsohon Gwamnan Jihar Osun ya yi ta’aziyyar rasuwar marigayi tsohon shugaban ƙasar Najeriya Muhammad Buhari, inda ya ayyana shi a matsayin wani Mala’ika ne da ya zo da jikin mutum, wanda ya bar tarihi a Najeriya.
Akande ya jagoranci tawagar manyan ƴan siyasa zuwa Kaduna domin yin ta’aziyya ga iyalan sa, yana mai bayyana damuwa ga rasuwar tsohon shugaban ƙasar.
Da yake bayyana ganin shi na ƙarshe na tsohon shugaban ƙasar a Daura, Bisi Akande ya gansa da lafiyar sa da ƙwarin sa, wanda ya nuna babu wata alamar rashin lafiya, wanda ya nuna mutuwa dole ce ga kowa.