Tsohon hadimin Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari me suna Babafemi Ojudu da yayi aikin bada shawara akan harkar siyasa a ofishin tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Buhari bai so Osinbajo ko Tinubu su zama shugaban Najeriya ba.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a wani gidan rediyo na yanar gizo me suna Edmund Obilo’s State Affairs.
Ya kuma ce zagayen neman delegates kadai bai isa ba su ci zabe inda yace kamata yayi ace shugaba Buhari ya baiwa hadimansa baki kan su taimakaw Osinbajo amma yaki.
Yace koda Tinubu ma yawa Buharin wayaune shiyasa ya samu nasara.