Shugabannin ƙwadago da na gwamnati na tattaunawa
Wakilan ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC na can na ci gaba da tattaunawa da wakilan gwamnati a ofishin sakataren gwamnati da ke Abuja.
Wannan dai na zuwa ne bayan kwashe sa'o'i da dama gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago suna yajin aiki a Najeriyar, inda asibitoci da makarantu da sauran ma'aikatu suka kasance a rufe.
Gwamnatin shugaba Tinubu ta nemi 'yan ƙungiyar da su janye yajin aikin su koma bakin tattaunawa.
Wannan tattaunawar ita ce zangon farko kafin wadda za a yi a ranar Talata.