Saturday, March 29
Shadow

Kiwon Lafiya

Yadda ake gwajin ciki da gishiri

Gwajin Ciki, Magunguna
Ana yin gwajin ciki da gishiri a gida dan gane ko mace na da ciki ko bata dashi. Yanda ake yinshi shine: Ana samun kofi ko mazubi a yi fitsari a ciki sai a zuba gishiri a ciki kamar chokali 2 zuwa 3. Sai a barshi zuwa minti 1 ko 5. Idan yayi ruwan madara ko yayi gudaji, to alamar mace na da ciki kenan. Idan kuma ya tsaya a yanda yake ba tare da ya canja ba to baki da ciki. Saidai shi wannan gwaji na gishiri bashi da inganci a wajen masana kiwon lafiya kuma babu wata hujja ta ilimi data tabbatar da sahihancinsa. Hanya mafi inganci da ake yin gwajin ciki itace ta hanyar zuwa Asibiti a gwada mace ko kuma amfani da tsinken gwaji wanda ake cewa pt strip test. Mun yi rubutu kan yanda ake yin wannan gwaji: Yadda ake amfani da tsinken gwajin ciki