
Rahotanni daga gidan yarin Maiduguri na cewa, Charles Oka da ake tsare dashi a gidan yarin saboda tayar da bam a ranar ‘yancin Najeriya ya mutu.
Rahoto a daren jiya daga Sahara reporters yace an jefa bam a dakin da Charles Okah ke tsare wanda hakan yasa hayaki ya tashi a dakin wuta ta tashi ta kama gidan sauron da yake ciki da kuma katifar da yake kwanciya akai.
A sabon rahoton da aka samu yau yace Charles Okah ya jikkata sanadiyyar wannan lamari.
Saidai daga baya an samu rahotanni dake cewa yana mutu amma ba’a hukumance ba.
Charles Okah dai ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Ministan harkokin cikin gida inda yake zargin aikata rashawa da cin hanci a gidan yarin.
Tun daga nanne dai aka sakashi a gaba.
Hukumar gidan yarin Najeriya tace babu wani bam da ya tashi a gidan yarin.