Sunday, March 16
Shadow

China za ta haramta tsawwala sadakin aure da bikin ‘almubazzaranci’

Gwamnatin ƙasar China ta ci alwashin kawar da al’adar tsawwala sadaki da kuma bikin wadaka da kuɗi.

Alwashin, wanda ya fito ta bakin jami’in gwamnati mai kula da lamurran yankunan karkara (Zhu Weidong), na zuwa ne bayan yawan aure da ake ɗaurawa a ƙasar ya ragu sosai a bara.

Hukumomi na ganin cewa sadaki mai yawa na dubban daloli da ake yankawa da kuma kayan aure masu yawa da ake buƙata daga wurin maza, na daga cikin abubuwan da ke hana maza yin aure.

Sai dai har yanzu hukumomin ba su ɗauki wani mataki kan dokar raba kaya bayan rabuwar aure, wadda ake ganin ta fifita maza.

Karanta Wannan  WATA SABUWA: Masu Shaidar Ɗan Ƙasa Ta NIN Ne Kaɗai Za Su Samu Shinkafa Mai Rangwamen Farashi Ta Gwamnatin Tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *