
Tsohon hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari watau Bashir Ahmed ya bayyana cewa ci gaban da jimullar tsaffin Shuwagabannin kasa, Olusegun Obasanjo da Marigayi, Umar Musa ‘Yar’adua da Goodluck Jonathan suka kawo bai kai wanda Buhari ya kawo ba a shekaru 8 da yayi yana mulki.
Bashir ya bayyana hakane a kafarsa ta Twitter inda yake mayar da martani akan maganar da wani shafin PDP yayi na cewa lokacin karshe da Najeriya ke da dadi inda shafin ya wallafa hotunan tsaffin shuwagabannin.
Saidai Bashir ya bayyana waccan magana da cewa, abin dariya ce.
Saidai da yawa sun yi ta mayar masa da martani kan lamarin.