Rahotanni sun bayyana cewa, Likitoci sun tabbatar da cutar Prostate Cancer grade 3 ta kama Firaiministan Israela, Benjamin Netanyahu.
Hakan ya haifar masa da cutar yoyon Fitsari.
Dalilin hakan ne yasa dole za’a yi masa tiyata.
Hakan yasa aka dage shari’ar da ake shirin yi akansa a kotu ta zargin rashawa da cin hanci.
Wasu dai na ganin cewa, wannan dabara ce da Benjamin Netanyahu yake yi an kawar da hankali akan Shari’ar tasa har maganar ta shirice.
Hakanan ko da yakin da Benjamin Netanyahu ke ta dagewa ake yi da kungiyar Hamas, ana ganin kamar yana yin wannan dagiya ne saboda ya gujewa zarge-zargen rashawa da cin hanci da ake masa da kuma tsawaita ranar yin zabe.