Friday, December 5
Shadow

DA ƊUMIƊUMINSA: Ɗan Gidan IBB Ya Ki Karɓar Sabon Muƙamin Shugaban Bankin Manoma Da Tinubu Ya Ba Shi

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Mohammed Babangida, ɗan tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya yi watsi da nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya masa a matsayin Shugaban Bankin Manoma na Najeriya (BOA).

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Mohammed ya bayyana rashin amincewarsa da muƙamin, yana mai cewa wasu dalilai na sirri da kuma tsare-tsaren kansa ne suka sa ya yanke shawarar kin karɓa, duk da girmansa.

Nadin nasa ya kasance cikin jerin sabbin nade-naden da shugaban ƙasa ke yi domin farfaɗo da harkokin noma da bunkasa rayuwar manoma a ƙasar nan. Sai dai wannan mataki da Mohammed ya ɗauka na watsi da mukamin ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta da cikin ‘yan siyasa.

Karanta Wannan  Na Gano cewa: Yawanci mazan Kano basa iya ciyar da matansu, sannan ana yiwa yara mata auren wuri>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Har yanzu babu wata sanarwa kai tsaye daga fadar shugaban ƙasa ko daga bakin Mohammed Babangida kansa kan dalilan da suka sa ya ƙi karɓar muƙamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *