DA ƊUMI-ƊUMINSA: A’isha Widad Ta Kafa Tarihin Zama Gwarzuwar Daliba.

A’isha Widad ’yar shekara 24, tana jami’a aka yi mata aure, ta samu juna biyu har ta haihu ta yi raino, kuma ba a cikin makaranta take zama ba, amma duk da haka ta kafa tarihin zama gwarzuwar ɗalibar da shekara 35 rabon da a samu mai irin sakamakon da kammala karatunta a fannin shari’a.