Thursday, January 15
Shadow

Da Duminsa: A karin Farko Musulmi ya zama magajin garin New York City, na kasar Amurka

Zohran Mamdani wanda musulmi ne ya ci zaben magajin garin New York City a kasar Amurka.

Wannan shine karin farko da hakan ta faru a tarihin Birnin Na New York, hakanan Zohran Mamdani dan Asalin kasar Uganda ne, daga baya ya je kasar Amirka ya zama dan kasa.

Zohran Mamdani ya kayar da tsohon gwamnan jihar New York Andrew Cuomo wanda Shugaban kasar, Donald Trump da Attajirin Duniya Elon Musk suka goyi baya.

A baya dai, Donald Trump yace idan Zohran Mamdani ya ci zaben magajin garin New York, zai dakatar da kudaden da gwamnatin tarayya ke aikawa birnin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Shima tsohon shugaban APC, Ganduje ya tafi Madina dan halartar jana'izar Dantata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *