
Rahotanni dake fitowa daga gabas ta tsakiya na cewa kasar Israyla ta kaiwa tashar Nùkiliya ta kasar Ìràn hari.
Rahoton yace harin ya kashe babban janar me kula da rundunar da ake kira Revolutionary Guard ko IRGC na kasar Iran me suna Janar Hossein Salami.
Kafofin yada labarai na kasar Iran din sun tabbatar da hakan.
Tashar talabijin ta kasar Iran ta nuna wasu gine-gine a kasar na ci da wuta bayan harin.
Kasar Israyla tace zata ci gaba da kaiwa Iran harin har sai ta nakasa shirinta na mallkar makamin kare dangi.