Tuesday, May 13
Shadow

Da Duminsa: A karshe dai, Sanata Natasha Akpoti ta baiwa Sanata Godswill Akpabio hakuri inda tace yanzu ta gane kurenta

Sanata Natasha Akpoti ta fito ta baiwa kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio hakuri kan zargin da ta masa na nemanta.

Saidai ta nemi hakurinne ta hanyar zunde da shagube.

A cikin wasikar data wallafa a shafinta na facebook.

Sanata Natasha ta ce cikin habaici tana baiwa Sanata Akpabio Hakuri.

Tace ta gano cewa nasarar dan majalisa a wani lokacin ba jajircewa da cacanta ce ke kawota ba amma biyayya ga bukatar wani.

Tace kaiconta da bata gane cewa ba kin bashi hadin kai abu ne da baya daya daga cikin dokokin da aka zayyana a majalisar.

Tace tana bayar da hakuri saboda girmama sanin aiki da hake hakkin mutanenta fiye da sharholiya a bayan fage.

Karanta Wannan  Idan Baku Daukar shawarwarin da muke bayarwa ba za'a kawo karshen matsalar tsaro ba a kasarnan>>Akpabio ya Gargadi Tinubu

Tace yanzu ta gane kuskurenta dan ta ga sakamakon abinda ta aikata inda ta gamu da tsaiko da fushi da nuna isa, dan haka yanzu ta kwantar da kai kasa.

Tace tana rokonshi ya yafe mata saboda ita ta yi amannar ta samu kujerarta ne ta hanyar zabe ba bin maza ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *