
Rahotanni sun tabbata cewa, shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga mukaminsa.
Jaridar Vanguard ta bayyana cewa ta samu tabbacin saukar Ganduje daga mukaminsa.
Babu tabbacin dalilin da yasa Ganduje ya sauka daga mukaminsa amma wata majiya daga jam’iyyar ta tabbatar da saukar Ganduje.
Rahotanni sun ce kamin saukarsa daga mukamin, an dauke duka wasu abubuwan sa daga ofishin shugaban jam’iyyar dake Abuja.