Thursday, December 25
Shadow

Da Duminsa: Abin ya zo, Kasar Amurka ta turo jirgin Leken Asiri Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa, Kasar Amurka ta aiko da jirgin saman Lekan Asiri zuwa Najeriya.

Jirgin kamar yanda me saka ido akan ayyukan masu ikirarin Jìhàdì a yankunan Sahel, Brant Philip ya bayyana, yace ya yi leken Asirin ne a Jihar Borno, Akan Kungiyar ÌSWÀP.

Jirgin ya taso ne daga matsugunin kasar Amurkar dake kasar Ghana.

Sahara Reporters ta ruwaito Brant Philip yana cewa Gwamnatin Najeriya ta amincewa kasar Amurkar ta kai hari kan ‘yan kungiyar.

Sannan yace Amurkar zata yi amfani da jihar Naija a matsayin matsuguninta yayin wannan aiki.

Saidai hadimin tsohon shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya soki Brant Philip inda yace bai kamata ya fitar da wannan bayani ba dan bayanine na sirri kuma kamar yana ankarar da ‘yan Kungiyar ÌŚWÀP dinne su shiryawa harin.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Gwagwaren Nijeriya Ku Shirya, Za Mu Fara Karbar Haraji Daga Wajen Ku Domin Rabawa Masu Iyalin Dake Fadin Kasar Nan, Inji Gwamnatin Tarayya, Ta Bakin Ministan Cikin Gida, Olubinmi Tunji-Ojo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *