Tuesday, December 16
Shadow

Da Duminsa: Akwai yiyuwar Najeriya zata iya kaiwa ga gasar cin kofin Duniya na 2026 duk da Dr. Congo ta cireta

Rahotanni sun bayyana cewa, har yanzu akwai yiyuwar Najeriya ta samu damar buga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026 wanda za’a yi a kasashen Amurka, Canada, da Mexico.

Hakan na zuwane bayan da hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta shigar da korafi a gaban hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA inda take cewa wasu daga cikin ‘yan wasan kasar Dr. Congo basu cancanci yi wa kasar wasa ba.

Korafin na cewa akalla 6 zuwa 9 na ‘yan wasan Dr. Congo sun koma ‘yan kasar ta Dr. Congo ne daga wasu kasashe daban-daban kuma ma har FIFA ta tantancesu ta amince da hakan.

Karanta Wannan  Allah Sarki: Bayan Shekaru 6 da watanni 3 a gidan yari an gano bashi da laifi

Saidai NFF sun gano cewa, daga cikinsu akwai wadanda basu bar kasashen su na baya ba, watau ma’ana suna rike da fasfon kasashe biyu, wanda kundin tsarin mulkin kasar Dr. Congo ya haramta rike fasfon kasashe Biyu.

Yanzu dai NFF na jiran hukuncin FIFA game da wannan korafi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *