
Rahotanni daga kasar Burkina Faso na cewa, Kasar zata Yankewa sojojin Najeriya 11 hukuncin daurin rai da rai idan ta samesu da laifin da take zarginsu da aikatawa.
Kasar dai ta kama sojojin Najeriya 11 da jirginsu me kirar C-130 ne bayan da ya ratsa ta kasar ba bisa Ka’ida ba.
Wani me sharhi akan Al’amuran yau da kullun ya bayyana cewa, kasar ta Burkina Faso zata gurfanar da sojojin Najeriyar a gaban kotu kuma idan aka samesu da laifi, zasu iya fuskantar Hukuncin daurin rai da rai.