Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: An sake dàukè wàsù ‘yàn Màtà 13 à Arèwà

Rahotanni sun tabbatar da cewa, an sake yin garkuwa da wasu ‘yan mata 13 a Arewa.

Lamarin ya farune a garin Mussa dake karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno.

Kakakin majalisar jihar, Rt. Hon. Abdullahi Askira ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yace daya daga cikin ‘yan matan da aka sace ta kubuta kuma an mayar da ita hannun iyayenta.

Ya kara da cewa, ‘yan matan na tsakanin shekaru 15 zuwa 20 ne inda yace har yanzu 12 na hannun ‘yan Bindigar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Masu yin aure da kananan shekaru ku daina, ku bari sai kun girma>>Inji Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma Wakili

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *