Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: An samu Matuka jirgin saman Air Peace da shaye-shayen abubuwan Maaye

Rahotanni daga hukumar bincike ta kasa, The Nigerian Safety Investigation Bureau sun bayyana cewa, an samu biyu daga cikin matuka jirgin saman kamfanin Air Peace da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Abubuwan da aka samesu da sha shine kwayoyi da kuma giya.

Hakan na zuwane bayan da jirgin da suke tukawa ya kaucewa hanya a filin jirgin samana na Fatakwal a ranar July 13, 2025.

Me magana da yawun hukumar binciken ta Najeriya, Mrs Bimbo Olawumi Oladeji ce ta tabbatar da hakan ga manema labarai na jaridar Punchng.

An gano cewa matuka jirgin sun yi wasa da rayuwar mutane 103 da suke dauke dasu a wancan lokacin.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta soke faretin bikin ranar dimokuraɗiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *