
Rahotanni daga Maiduguri na cewa wani abin fashewa me kama da bam ya fashe a gidan yarin dake garin da daren Ranar Lahadi.
Lamarin ya farune da misalin karfe 9 na darennan inda hakan yayi sanadiyyar tashin wuta a dakin da ake tsare da Charles Okah.
Wasu shaidu sun ce an cilla wani abu me kama da bam a dakin da ake tsare da Charles Okah din inda aka ga hayaki na tashi.
Wannan lamari ya biyo bayan budaddiyar wasikar da Charles Okah ya aikewa ministan harkokin cikin gida, Olubunmi-Ojo ne inda yake korafi kan yawaitar cin hanci a gidajen yarin Maidugurin.
Rahoton na Sahara reporters yace Okah ya rika tari inda aka ji yana fadin an cilla masa bom a dakinsa.
Saidai babu wanda ya kai masa dauki dan kuwa a cewar rahoton ma’aikatan gidan yarin dake aikin dare basa nan.
Hakanan wannan lamari zai iya jefa rayuwar wadanda ke kwance a Asibitin gidan yarin cikin matsala wanda hakan ana tsammanin zai iya kaiwa ga balla gidan yarin.
Ana tunanin dai kamin a kai dauki wata kila sai da Asuba.
Hakanan rahoton yace an nemi naurar karta kwana ta kashe Gibara an rasa a cikin gidan yarin.