
Rahotannin dake fitowa daga kasar Amurka na cewa, Mataimakin shugaban kasar, JD. Vance ya fasa kai ziyarar da yayi niyya zuwa kasar Israela.
An bayyana cewa rashin jin dadin fadada hare-haren Israyla a Gaza ne yasa JD. Vance daukar wannan mataki.
Dama dai a baya hutudole.com ya kawo muku rahoton cewa, Amurka na shirin amincewa da kafuwar kasar Palasdinu saboda an samu rashin jituwa tsakanin kasashen Biyu.
Trump dai bai san ana juyashi yayin da rahotanni ke cewa, shi kuma shugaban Israela Benjamin Netanyahu yana son ya rika juya shuwagabannin Amurka.