
Matatar Man fetur ta Dangote ta sake sanar da kara rage farashin Man fetur dinta inda a yanzu take sayarwa ga masu sari akan 835 kan kowace Lita maimakon 865 kan kowace Lita da ake sayarwa a baya.
A ranar Laraba ne dai matatar man ta sanar da abokan huldarta da rage wannan sabon farashin.
Wannan ne karo na 3 da matatar man ta Dangote ke rage farashin man ta a cikin makonni 6 da suka gabata.