Friday, December 26
Shadow

Da Duminsa: Fadar Shugaban kasa tace Sojoji da DSS sun kira Tshàgyèràn Dhàjì suka ce su saki mutanen da suka yì Ghàrkùwà dasu a coci kuma sun sake su din

Fadar Shugaban kasa ta tabbatar da cewa, DSS da sojoji sun kira ‘yan Bìndìgà da suka yi garkuwa da mutanen cocin Eruku, dake karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara suka ce su sakesu.

Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi dashi a Arise TV.

Yace Jami’an tsaron sun kira ‘yan Bindigar suka ce su saki mutanen da suka sace a cocin kuma suka sakesu saboda sun san rashin sakinsu ko rashin yiw Gwamnati biyayya sakamakon da zai zo musu dashi.

Yace mataki na gaba da jami’an tsaron zasu dauka wannan kuma sirri ne.

Hakanan yace a lokuta da dama jami’an tsaron kan samu bayanin inda ‘yan Bindigar suke amma saboda gudun kada harin da zasu kai ya shafi wadanda ake rike dasu shiyasa basu cika Afkawa Tshàgyèràn Dhàjìn ba.

Karanta Wannan  Yawan 'yan majalisar APC ya karu a majalisar tarayya bayan canja sheka da 'yan PDP da Labour party da NNPP suka yi ta yi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *