
Rahotanni da muke samu a yanzu haka na cewa, Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA ta karbi korafin Najeriya akan Dr. Congo kuma tace tana bincike akan lamarin.
Najeriya ta shigar da korafin cewa, kasar Dr. Congo ta yi amfani da ‘yan wasa masu kasashe biyu a wasan da suka buga da Najeriya wanda hakan ya sabawa dokar kasar.
Idan Najeriya ta yi nasara a wannan Shari’ar, akwai yiyuwar zata buga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026.