Rahotanni da muke samu na cewa Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya kara kudin man fetur.
Rahotan yace a yanzu sabon farashin man ya kai Naira 1060 akan kowace lita a Abuja inda kuma a Legas ake sayansa akan Naira 1025 akan kowace lita.
Makonni 3 da suka gabata ne dai kamfanin na NNPCL ya kara farashin man fetur din zuwa 1030 akan kowace lita.
Hakan na zuwane bayan da shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya baiwa ‘yan Najeriya zabin sayen man fetur akan Naira 1000 ko su koma amfani da CNG wanda ake saye akan Naira 200 kan kowace lita.