Friday, December 26
Shadow

Da Duminsa: Gwamnatin Jihar Kano ta dauki mataki akan Malam Lawal Triumph, saidai bai yiwa dalibansa dadi ba

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa’azi

Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ta sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi.

A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma’aiki.

A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura.

Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Likafa ta yi gaba inda aka ga Iftihal Madaki a karo na biyu tana rawa da Soja Boy

Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da son rai ko rashin adalci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *