Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Gwamnatin tarayya ta soke harajin kaso 5 na kamfanonin Sadarwa wanda yasa kudin data dana kira suka kara tsada

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta soke harajin Kaso 5 cikin 100 na kamfanonin sadarwa wanda yasa kudin data dana kiran waya suka kara tsada.

Hakan na zuwane daga bakin shugaban hukumar sadarwa ta kasa, NCC, Dr. Aminu Maida inda yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya bayar da umarnin a yi hakan.

Yace shugaban ya yi hakan ne dan saukakawa ‘yan Najeriya da suka fuskanci tsadar kudin kira dana data.

Harajin dai tun bayan kaddamar dashi aka kara kudin kira dana data da kaso 50 cikin 100.

Hakanan jaridar Punchng tace tun a lokacin mulkin Buhari ne aka gabatar da wannan haraji wanda ya samu suka daga kamfanonin sadarwa da masu amfani da wayoyi.

Karanta Wannan  Matsalar tsaron kasarnan ta fi karfin jami'an tsaron mu, ba zasu iya ba>>Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *