
Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta sanar da dakatar da sufurin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, har sai abinda hali yayi.
Hukumar ta sanar da hakane jim kadan bayan hadarin da aka samu bayan tashin jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna bayan da ya kaucewa taragonsa.
Daraktan hukumar, Kayode Opeifa ne ya sanar da haka a Abuja ga manema labarai, Ya musanta rade-radin da ake yi cewa dama jirgin kasan yana da matsala.
Yace jami’an hukumar su dana hukumar bincike ta kasa, (NSIB) sun halarci wajan faruwar hadarin inda yace suna kan bincike kan lamarin.
Ya kuma kara da cewa, sun fara shirin mayarwa da fasinjojin fake cikin jirgin kudaden tikiti da suka saya.
Yace mutane 6 sun ji raunika ba masu muni ba kuma an basu kulawar data kamata.