Friday, December 26
Shadow

Da Duminsa: Ji Abinda mataimakin Gwamnan Bauchi yace bayan da “ya zabgawa Minista mari”

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Muhammad Jatau ya yi magana akan rahoton dake cewa ya zabgawa ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Maitama Tuggar mari.

Jatau yayi magana ta bakin kakakinsa, Muslim Lawal inda yace rahoton marin ba gaskiya bane

Yace su basu ma da labari game da maganar marin a bakin ‘yan jarida suke ji.

Yace babu ta yadda za’a yi mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya mari minista, yace ko gwamna ba zai mari minista ba ballantana mataimakinsa.

Kokarin jin ta bakin ministan ya ci tura.

Karanta Wannan  Bayan da ya sha matsa a hannun DSS, Shugaban Kungiyar daliban Najeriya a karshe ya yadda ya karyata kansa kan zargin da yawa dan shugabab kasa, Seyi Tinubu cewa ya sa an masa dukan kawo wuka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *