
Jam’iyyar ADC na shirin shigar da Akalla Gwamnoni 5 cikinta kamin nan da zaben shekarar 2027.
Wata majiya tace ADC zata yi amfani da rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP dan jawo wasu gwamnonin jam’iyyar cikinta.
Manyan ‘yan siyasa su Atiku Abubakar da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Rotimi Amaechi da David Mark, Da John Oyegun da su Peter Obi, da sauransu da yawa sun shiga jam’iyyar ADC.
Gwamnonin da zasu koma ADC din tuni suka amince da wannan tayin inda suka ce amma a jira suka ga karshen rikicin Wike tukuna.
Hakanan majiyar tace akwai gwamnonin APC da suma suna tare da tafiyar APC amma basu fito sun bayyana kansu ba.
Hakanna wata majiyar tace ana kan tattaunawa da wasu karin Gwamnoni 7 da ke shirin shiga jam’iyyar ta ADC.
Gwamnonin dai sun fito ne daga jihohin Arewa da kudu, kamar yanda sanarwar ta tabbatar.